Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

W. W. 2:3-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Kamar yadda itacen gawasa yake a cikin itatuwan jeji,Haka ƙaunataccena yake a cikin sauran maza.Da farin ciki na zauna a inuwarsa,Ina jin daɗin halinsa ƙwarai.

4. Ya kai ni babban ɗakin da ake liyafa,Ƙauna ita ce tutarsa a gare ni.

5. Ka ciyar da ni da wainar zabibi,Ka ba ni 'ya'yan gawasa in sha in wartsake!Gama na cika da sha'awarka.

6. Bari ka ta da kaina da hannun hagunka,Ka rungume ni da hannun damanka.

7. Ku 'yan matan Urushalima,Ku rantse da bareyi, da batsiyoyi,Ba za ku shiga tsakaninmu ba,Ku bar ta kurum.

8. Na ji muryar ƙaunataccena!Ya zo a guje daga kan tuddai,Ya sheƙo daga tuddai zuwa wurina.

9. Ƙaunataccena kamar barewa yake,Kamar sagarin kishimi.Ga shi can, yana tsaye a bayan katangarmu.Yana leƙe ta tagogi,Yana kallona ta cikin asabari.

10. Ƙaunataccena ya yi magana da ni.Tashi mu tafi, ƙaunatacciyata, kyakkyawa.

11. Gama lokacin sanyi ya wuce,Ruwa kuma ya ɗauke.

12. Furanni suna hudowa a itatuwa ko'ina.Lokacin raira Waƙoƙi ya yi,Lokacin da kurciyoyi suke kuka ya yi.

Karanta cikakken babi W. W. 2