Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 4:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Sa'an nan Bo'aza ya ce wa dattawan da dukan jama'ar da suke wurin, “Yau ku ne shaidu, cewa, na sayi dukan abin da yake na Elimelek, da na Kiliyon, da na Malon daga hannun Na'omi.

10. Game da wannan kuma Rut, mutuniyar Mowab, matar marigayi Malon, ta zama matata domin in wanzar da sunan marigayin cikin gādonsa, don kada sunansa ya mutu daga na 'yan'uwansa, da kuma a garinsu. Ku ne fa shaidu a yau.”

11. Dukan jama'a suka ce, “Mu ne shaidu, Ubangiji yă sa matar da za ta zo gidanka ta zama kamar Rahila da Lai'atu waɗanda suka gina gidan Isra'ila. Allah ya arzuta ka cikin Efrata, yă sa ka yi suna a cikin Baitalami,

12. gidanku kuma ya zama kamar gidan Feresa, wanda Tamar ta haifa wa Yahuza, saboda 'ya'yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace.”

13. Bo'aza kuwa ya auri Rut, ta zama matarsa. Ya kuma shiga wurinta, Ubangiji kuwa ya sa ta yi ciki, ta haifa masa ɗa.

14. Sai mata suka ce wa Na'omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, da bai bar ki bā dangi na kusa ba, Allah ya sa ɗan ya yi suna a cikin Isra'ila.

15. Ya zama mai sanyaya miki rai, mai goyon tsufanki, gama surukarki wadda take ƙaunarki, wadda ta fiye miki 'ya'ya maza bakwai, ita ta haife shi.”

16. Sa'an nan Na'omi ta ɗauki yaron ta rungume shi a ƙirjinta, ta zama mai renonsa.

Karanta cikakken babi Rut 4