Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 4:14-18-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. Sai mata suka ce wa Na'omi, “Yabo ya tabbata ga Ubangiji, da bai bar ki bā dangi na kusa ba, Allah ya sa ɗan ya yi suna a cikin Isra'ila.

15. Ya zama mai sanyaya miki rai, mai goyon tsufanki, gama surukarki wadda take ƙaunarki, wadda ta fiye miki 'ya'ya maza bakwai, ita ta haife shi.”

16. Sa'an nan Na'omi ta ɗauki yaron ta rungume shi a ƙirjinta, ta zama mai renonsa.

17. Mata, maƙwabta kuwa suka ce, “An haifa wa Na'omi ɗa!” Suka raɗa masa suna Obida, shi ne mahaifin Yesse, uban Dawuda.

18-22. Wannan shi ne asalin zuriyar Dawuda. Aka fara daga Feresa zuwa Dawuda. Feresa ne mahaifin Hesruna, Hesruna kuma ya haifi Arama, Arama ya haifi Amminadab, Amminadab kuma ya haifi Nashon, Nashon ya haifi Salmon, Salmon kuma ya haifi Bo'aza, Bo'aza ya haifi Obida, Obida kuma ya haifi Yesse, sa'an nan Yesse ya haifi Dawuda.

Karanta cikakken babi Rut 4