Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Rut 3:1-6 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wata rana, Na'omi ta ce wa Rut, “'Yata, ya kamata in nemar miki miji don ki sami gida inda za ki huta, ki ji daɗi.

2. Bo'aza wanda kika yi aiki da barorinsa danginmu ne. Ga shi, zai tafi sussukar sha'ir a masussuka da maraice.

3. Sai ki yi wanka, ki shafa man ƙanshi, ki yafa tufafinki na ado, ki tafi masussukar, amma kada ki bari ya san zuwanki, sai bayan da ya riga ya ci ya sha.

4. Sa'ad da ya kwanta, sai ki lura da inda ya kwanta, sa'an nan ki tafi, ki buɗe mayafinsa a wajen ƙafafunsa, ki kwanta a ciki. Zai kuwa faɗa miki abin da za ki yi.”

5. Rut ta amsa, “Zan yi dukan abin da kika faɗa.”

6. Rut kuwa ta gangara zuwa masussukar, ta yi yadda surukarta ta faɗa mata.

Karanta cikakken babi Rut 3