Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Oba 1:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Isuwa, wato Edom, ga taskarka,An washe ta ƙaƙaf!

7. Waɗanda kake amana da su,Za su kore ka daga ƙasarka.Mutanen da suke amana da kai,Za su yaudare ka,Su ci ka da yaƙi.Abokan nan naka da kake ci tare dasu za su kafa maka tarko,Sa'an nan su ce, ‘Ina dukan wayonnan nasa?’ ”

8. Ni Ubangiji na ce, “A ranar da zanhukunta Edom,Zan hallaka masu hikimarka,Zan shafe hikima daga dutsenIsuwa.

9. Jarumawanka za su firgita, yaTeman,Za a kashe kowane mutum dagadutsen Isuwa.

10. “Saboda kama-karyar da ka yi waYakubu ɗan'uwanka,Za a sa ka ka sha kunya,Za a hallaka ka har abada.

11. A ranan nan ka tsaya kawai,A ranar da abokan gāba suka fasaƙofofinsa.Suka kwashe dukiyarsa,Suka jefa kuri'a a kan Urushalima.Ka zama kamar ɗaya daga cikinsu.

Karanta cikakken babi Oba 1