Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Oba 1:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Annabcin Obadiya ke nan.Wannan shi ne abin da Ubangiji Allah ya ce a kan al'ummar Edom.Ubangiji ya aiki manzonsa wurinsauran al'umma,Mun kuwa ji saƙonsa cewa,“Ku zo! Mu tafi mu yi yaƙi daEdom!”

2. Ubangiji ya ce wa al'ummar Edom,“Zan maishe ki ƙanƙanuwa a cikinsauran al'umma,Za a raina ki ƙwarai.

3. Girmankanki ya yaudare ki,Kina zaune a kagara, a kan dutse,Wurin zamanki yana canƙwanƙolin duwatsu.Don haka a zuciya kike cewa,‘Wa zai saukar da ni ƙasa?’

4. Ko da yake kina shawagi can samakamar gaggafa,Gidanki kuma yana can cikin taurari,Daga can zan saukar da ke,” in jiUbangiji

Karanta cikakken babi Oba 1