Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 9:11-22 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Ka yi hanya ta cikin teku domin jama'arka,Ka sa su bi ta ciki a kan sandararriyar ƙasa.Ka sa waɗanda suke fafararsu suka hallaka cikin zurfin teku,Suka nutse kamar dutse.

12. Da rana ka bishe su da al'amudin girgije,Da dare ka bishe su da al'amudin wuta.

13. Ka kuma sauka a bisa Dutsen Sinai,Ka yi magana da jama'arka a can,Ka ba su ka'idodin da suka dace,Da dokoki, da kyakkyawar koyarwa.

14. Ka koya musu su kiyaye Asabar ɗinka tsattsarka,Ka kuma ba su dokokinka ta hannun Musa bawanka.

15. Ka ba su abinci daga sama sa'ad da suka ji yunwa,Ruwa kuma daga dutse sa'ad da suka ji ƙishi,Ka faɗa musu su shiga su mallaki ƙasar da ka yi alkawari za ka ba su.

16. Amma kakanninmu suka yi fāriya, suka taurare,Suka ƙi yin biyayya da umarnanka.

17. Suka ƙi yin biyayya,Suka manta da dukan abin da ka yi,Suka manta da al'ajaban da ka aikata.Cikin fāriyarsu suka zaɓi shugaba,Don su koma cikin bauta a Masar.Amma kai Allah ne mai gafartawa,Kai mai alheri ne, mai ƙauna,Jinƙanka da girma yake, ba ka yashe su ba.

18. Ko sa'ad da suka yi wa kansu ɗan marakin zubi,Suka ce shi ne allahn da ya fisshe su daga Masar,Ai, sun yi maka ɓatanci, ya Ubangiji.

19. Amma ba ka rabu da su a hamada ba,Saboda jinƙanka mai girma ne.Ba ka kuwa kawar da girgije da wuta ba,Waɗanda suke nuna musu hanya dare da rana.

20. Ta wurin alherinka ka faɗa musu abin da ya kamata su yi,Ka ciyar da su da manna, ka ba su ruwa su sha.

21. Ka taimake su a jeji shekara arba'in,Ka ba su dukan abin da suke bukata,Ƙafafunsu ba su kumbura su yi musu ciwo ba.

22. “Ka sa sun ci al'ummai da mulkoki da yaƙi,Ƙasashen da suke maƙwabtaka da tasu.Suka ci ƙasar Sihon, Sarkin Heshbon,Da ƙasar Bashan, inda Og yake sarki.

Karanta cikakken babi Neh 9