Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 6:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sa'ad da fa aka sanar da Sanballat, da Tobiya, da Geshem Balarabe, da sauran abokan gābanmu, cewa na gina garun, har ba sauran tsaguwa da ta ragu, ko da yake a lokacin ban riga na sa wa ƙofofi ƙyamare ba,

2. sai Sanballat da Geshem suka aika wurina cewa, “Ka zo mu sadu a wani ƙauye a filin Ono,” amma da nufin su cuce ni.

3. Sai na aika musu da manzanni, na ce, “Ina fama da babban aiki, ba ni da damar zuwa wurinku. Don me zan bar aiki in gangaro zuwa wurinku?”

4. Suka yi ta aiko mini da wannan saƙo har sau huɗu, ni kuwa na yi ta ba su amsa irin ta dā.

5. A karo na biyar sai Sanballat ya aiko da buɗaɗɗiyar wasiƙa ta hannun baransa, da irin maganar dā.

6. Ga abin da yake cikin wasiƙar, “Geshem ya faɗa mini, ana ta ji jita jita wurin maƙwabta, cewa kai da Yahuduwa kuna niyyar tayarwar, don haka kake ginin garun, kana so kuma ka naɗa kanka sarki.

7. Ga shi, ka sa annabawa su yi shelarka a Urushalima cewa, ‘Akwai sarki a Yahuza.’ To, za a faɗa wa sarki wannan magana, sai ka zo mu yi shawara tare a kan wannan al'amari.”

8. Sai na mayar masa da amsa cewa, “Faufau, ba a yi wani abu haka kamar yadda ka faɗa ba, kai ne ka ƙaga wannan a zuciyarka.”

Karanta cikakken babi Neh 6