Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 5:9-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Na kuma ce musu, “Abin da kuke yi ba shi da kyau. Ya kamata ku yi tsoron Allah don ku hana al'ummai, abokan gabanmu, yi mana ba'a.

10. Ni ma da 'yan'uwana da barorina muna ba da rancen kuɗi da hatsi. Sai mu daina sha'anin ba da rance da ruwa.

11. Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”

12. Sa'an nan suka ce, “Za mu mayar musu da waɗannan abubuwa, ba kuwa za mu bukaci wani abu a gare su ba. Za mu yi abin da ka faɗa.”Sai na kira firistoci su rantsar da su, cewa za su yi yadda suka alkawarta.

13. Sai kuma na kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, ya wofintar da shi.”Sai dukan taron suka amsa, “Amin, amin.” Suka kuma yabi Ubangiji. Suka kuwa cika alkawarin da suka yi.

14. Tun kuma lokacin da na yi mulkin ƙasar Yahuza, a shekara ta ashirin zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Artashate, shekara goma sha biyu ke nan, ni ko 'yan'uwana, ba wanda ya karɓi albashin da akan ba mai mulki.

15. Waɗanda suka riga ni mulki sun nawaita wa mutane. Sun yi ta karɓar abinci da ruwan inabi daga gare su, banda shekel arba'in kowace rana domin abinci da ruwan inabi. Har ma barorin masu mulki sun nawaya wa mutane. Amma ni ban yi haka ba, saboda ina tsoron Allah.

16. Na mai da hankali ga aikin garu, ban samar wa kaina gonaki ba. Barorina duka suka haɗa kai da ni a kan aikin gini.

17. Duk da haka akwai Yahudawa da shugabanni ɗari da hamsin waɗanda suke cin abinci a teburina, banda waɗanda sukan zo wurinmu daga al'umman da suke kewaye da mu.

18. Ga abincin da ake shiryawa kowace rana, sa ɗaya, da tumaki shida kyawawa, da kuma kaji. A kowace rana ta goma akan kawo salkunan ruwan inabi masu yawa, amma duk da haka ban karɓi albashin da akan ba mai mulki ba, domin wahala ta yi wa mutane yawa.

19. Ya Allahna, ka tuna da alherin da na yi wa mutanen nan.

Karanta cikakken babi Neh 5