Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 5:7-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Sai na yi shawara a zuciyata, na yi wa manya da shugabanni faɗa, na ce musu, “Kuna musguna wa 'yan'uwanku da yake kuna ba su rance da ruwa.”Sa'an nan na kira babban taro saboda su.

8. Na ce musu, “Da iyakacin ƙoƙarinmu mun fanshi 'yan'uwanmu Yahudawa waɗanda aka sayar wa al'ummai, amma ga shi, kuna tilasta wa 'yan'uwanku su sayar da kansu ga 'yan'uwansu.” Sai suka yi tsit, suka rasa abin da za su ce.

9. Na kuma ce musu, “Abin da kuke yi ba shi da kyau. Ya kamata ku yi tsoron Allah don ku hana al'ummai, abokan gabanmu, yi mana ba'a.

10. Ni ma da 'yan'uwana da barorina muna ba da rancen kuɗi da hatsi. Sai mu daina sha'anin ba da rance da ruwa.

11. Yau sai ku mayar musu da gonakinsu, da gonakin inabinsu, da na zaitunsu, da gidajensu, da kashi ɗaya bisa ɗari na kuɗi, da na hatsi, da na ruwan inabi, da na mai, waɗanda kuka karɓa a wurinsu.”

12. Sa'an nan suka ce, “Za mu mayar musu da waɗannan abubuwa, ba kuwa za mu bukaci wani abu a gare su ba. Za mu yi abin da ka faɗa.”Sai na kira firistoci su rantsar da su, cewa za su yi yadda suka alkawarta.

13. Sai kuma na kakkaɓe hannuna, na ce, “Duk wanda ya karya wannan alkawari, haka Allah zai kakkaɓe shi daga gidansa da aikinsa. Allah zai kakkaɓe shi, ya wofintar da shi.”Sai dukan taron suka amsa, “Amin, amin.” Suka kuma yabi Ubangiji. Suka kuwa cika alkawarin da suka yi.

14. Tun kuma lokacin da na yi mulkin ƙasar Yahuza, a shekara ta ashirin zuwa shekara ta talatin da biyu ta sarautar sarki Artashate, shekara goma sha biyu ke nan, ni ko 'yan'uwana, ba wanda ya karɓi albashin da akan ba mai mulki.

Karanta cikakken babi Neh 5