Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 13:14-21 Littafi Mai Tsarki (HAU)

14. “Ka tuna da ni, ya Allahna, saboda wannan. Kada ka manta da ayyukan kirki da na yi a Haikalin Allah da kuma na hidimarsa.”

15. A kwanakin nan na ga mutane a Yahuza suna matse ruwan inabi, suna labta wa jakunansu buhunan hatsi, da ruwan inabi, da 'ya'yan inabi, da ɓaure, da kaya iri iri, suna kawo su cikin Urushalima a ran Asabar. Sai na yi musu faɗa a kan sayar da abinci a wannan rana.

16. Mutanen Taya da suke zaune a birnin sukan kawo kifi da kaya iri iri, su sayar wa mutanen Yahuza a Urushalima a ranar Asabar.

17. Sai na tsauta wa manyan mutanen Yahuza, na ce musu, “Wane irin mugun abu ne kuke yi haka, kuna ɓata ranar Asabar?

18. Ashe, ba haka kakanninku suka yi ba, har wannan ya sa Allahnmu ya kawo mana masifa, mu da dukan birnin? Duk da haka kuna ƙara kawo wa Isra'ila hasala saboda kuna ɓata ranar Asabar.”

19. Magariba na yi kafin ranar Asabar, sai na yi umarni a rufe ƙofofin Urushalima, kada a buɗe su sai Asabar ta wuce. Na sa waɗansu barorina a ƙofofin, don kada su bari a shigo da kaya ran Asabar.

20. Sau ɗaya ko sau biyu, 'yan kasuwa da masu sayar da abubuwa iri iri suka kwana a bayan Urushalima.

21. Amma na tsauta musu, na ce, “Me ya sa kuka kwana a bayan garu? Idan kun ƙara yin haka zan kama ku.” Tun daga wannan lokaci ba su ƙara zuwa a ranar Asabar ba.

Karanta cikakken babi Neh 13