Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Neh 12:38-47 Littafi Mai Tsarki (HAU)

38. Ƙungiyar jama'a ta biyu ta masu yin waƙoƙin godiya, ta bi ta wajen hagu. Na bi su tare da rabin jama'a a kan garu, sama da Hasumiyar Tanderu zuwa garu mai fādi,

39. da Kuma sama da Ƙofar, Ifraimu da wajen Tsohuwar Ƙofar, da wajen Ƙofar Kifi, da Hasumiyar Hananel, da Hasumiyar Ɗari zuwa Ƙofar Tumaki, sai suka tsaya a Ƙofar Tsaro.

40. Haka fa ƙungiyoyi biyu ɗin nan masu raira waƙoƙin godiya suka tsaya a Haikalin Allah.Ni da rabin shugabanni muna tare da su.

41. Tare da firistoci kuma, wato su Eliyakim, da Ma'aseya, da Miniyamin, da Mikaiya, da Eliyehoyenai, da Zakariya, da Hananiya, suna busa ƙaho,

42. da kuma Ma'aseya, da Shemaiya, da Ele'azara, da Uzzi, da Yehohanan, da Malkiya, da Elam, da Ezer, suna raira waƙoƙi, Yezrahiya kuma shi ne shugabansu.

43. Jama'a suka miƙa hadayu da yawa a wannan rana, suka yi murna, gama Allah ya faranta musu zuciya ƙwarai. Mata da yara kuma suka yi murna. Aka ji muryar murnar mutanen Urushalima daga nesa.

44. A ran nan aka sa mutanen da za su lura da ɗakunan ajiya, da sadakoki, da nunan fari, da zaka. Su ne za su tara nunan fari daga gonakin da suke kusa da garuruwa, bisa ga yadda doka ta ce, saboda firistoci da Lawiyawa, gama mutanen Yahuza sun yi murna saboda hidimar da firistoci da Lawiyawa suka yi.

45. Sun yi wa Allahnsu sujada, sun yi hidimar tsarkakewa tare da mawaƙa da masu tsaron ƙofofi kamar yadda Dawuda da ɗansa Sulemanu suka umarta.

46. A dā a zamanin Dawuda da Asaf akwai shugaban mawaƙa, akwai kuma waƙoƙin yabo da na godiya ga Allah.

47. A zamanin Zarubabel da zamanin Nehemiya dukan jama'ar Isra'ila suka biya wa mawaƙa da masu tsaron ƙofofi bukatarsu ta kowace rana. Sun kuma ba Lawiyawa sadokoki, su Lawiyawa kuma suka ba zuriyar Haruna nasu rabo.

Karanta cikakken babi Neh 12