Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Nah 3:10-15 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Duk da haka an tafi da ita, an kai tacikin bauta.An fyaɗa ƙanananta a ƙasa,An yi kacakaca da su a kowacemararraba.An jefa kuri'a a kan manyanmutanenta,Aka ɗaure dukan manyan mutanentada sarƙoƙi.

11. Ke Nineba kuma za ki bugu,Za a ɓoye ki.Za ki nemi mafaka a wurin maƙiyinki.

12. Dukan kagaranki suna kama daitatuwan ɓaure,Waɗanda 'ya'yansu suka harba.Da an girgiza sai su faɗo a bakin maisha.

13. Sojojinki kamar mata suke atsakiyarki!An buɗe wa maƙiyanki ƙofofinƙasarki.Wuta za ta cinye madogaranƙofofinki.

14. Ki tanada ruwa domin za a kewayeki da yaƙi!Ki ƙara ƙarfin kagaranki!Ki tafi kududdufi, ki kwaɓa laka!Ki ɗauki abin yin tubali!

15. A can wuta za ta cinye ki,Takobi zai sare ki,Zai cinye ki kamar fara.Ki riɓaɓɓanya kamar fara.Ki kuma riɓaɓɓanya kamar ɗango.

Karanta cikakken babi Nah 3