Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mika 5:4-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Shi kuwa zai tashi ya ciyar dagarkensa da ƙarfin Ubangiji,Da ɗaukakar sunan UbangijiAllahnsa.Za su kuwa zauna lafiya,Gama zai zama mai girma cikinduniya duka.

5. Zai zama salamarmu.Sa'ad da kuma Assuriyawa za sukawo mana yaƙi,Za su tattake kagaranmu,Za mu sa makiyaya bakwai dashugabanni takwas su yi gāba dasu.

6. Za su mallaki ƙasar Assuriya datakobi,Su shiga ƙofofin ƙasar Nimrod dazararren takobi,Zai cece mu daga hannunBa'assuriye,Sa'ad da ya kawo wa ƙasarmuyaƙi,Sa'ad da kuma ya tattake ƙasarmu.

7. Sa'an nan ringin Yakubu zai zamarwa mutaneKamar raɓa daga wurin Ubangiji,Kamar kuma yayyafi a kan tsire-tsire,Wanda ba ya jinkiri ko ya jiramutane.

8. Ringin Yakubu kuma zai zamar waal'umman duniya,Kamar yadda zaki yake a tsakaninnamomin jeji,Kamar kuma yadda zaki yake atsakanin garkunan tumaki,Wanda, sa'ad da ya ratsa, yakantattaka,Ya yi kacakaca da su,Ba wanda zai cece su.

9. Za a ƙarfafa hannunka a kanmaƙiyanka,Za a datse maƙiyanka duka.

10. “A wannan rana, ni Ubangiji na ce,Zan kashe dawakanku, in hallakakarusanku.

11. Zan shafe biranen ƙasarku,In rushe garunku.

Karanta cikakken babi Mika 5