Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 1:9-16 Littafi Mai Tsarki (HAU)

9. Ƙazantarta tana cikin tufafinta,Ba ta tuna da ƙarshenta ba,Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce,Ba ta da mai yi mata ta'aziyya.“Ya Ubangiji, ka dubi wahalata,Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”

10. Maƙiyi ya miƙa hannunsaA kan dukan kayanta masu daraja,Gama ta ga al'ummai sun shiga Haikali,Su waɗanda ka hana su shiga cikin jama'arka.

11. Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci,Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinciDon su rayu.“Ya Ubangiji ka duba, ka gani,Gama an raina ni.”

12. “Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku?Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa,Wanda Ubangiji ya ɗora mini,A ranar fushinsa mai zafi.

13. “Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana.Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta,Ya komar da ni baya,Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.

14. “Ubangiji ya tattara laifofinaYa yi karkiya da su,Ya ɗaura su a wuyana,Ya sa ƙarfina ya kāsa.Ya kuma bashe ni a hannunWaɗanda ban iya kome da su ba.

15. “Ubangiji ya yi watsi da majiya ƙarfina,Ya kirawo taron jama'a a kainaDon su murƙushe samarina.Ya kuma tattake Urushalima, zaɓaɓɓiyarsa,Kamar 'ya'yan inabi a wurin matsewa.

16. “Ina kuka saboda waɗannan abubuwa,Hawaye suna zuba sharaf-sharaf daga idanuna.Gama mai ta'azantar da ni,Wanda zai sa in murmure yana nesa da ni.'Ya'yana sun lalace,Gama maƙiyi ya yi nasara!”

Karanta cikakken babi Mak 1