Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 1:6-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Dukan darajar Sihiyona ta rabu da ita,Shugabanninta sun zama kamar bareyinDa ba su sami wurin kiwo ba,Suna gudu ba ƙarfi a gaban wanda yake korarsu.

7. A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama,Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā.A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi,Ba wanda ya taimake ta,Maƙiyanta sun gan ta,Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.

8. Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske,Saboda haka ta ƙazantu,Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina taDomin sun ga tsiraicinta,Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.

9. Ƙazantarta tana cikin tufafinta,Ba ta tuna da ƙarshenta ba,Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce,Ba ta da mai yi mata ta'aziyya.“Ya Ubangiji, ka dubi wahalata,Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”

10. Maƙiyi ya miƙa hannunsaA kan dukan kayanta masu daraja,Gama ta ga al'ummai sun shiga Haikali,Su waɗanda ka hana su shiga cikin jama'arka.

11. Dukan jama'arta suna nishi don neman abinci,Sun ba da kayansu masu daraja saboda abinciDon su rayu.“Ya Ubangiji ka duba, ka gani,Gama an raina ni.”

12. “Dukanku masu wucewa, ba wani abu ba ne a gare ku?Ku duba, ku gani, ko akwai baƙin ciki irin nawa,Wanda Ubangiji ya ɗora mini,A ranar fushinsa mai zafi.

13. “Daga sama ya aukar da wuta a cikin ƙasusuwana.Ya kuma kafa wa ƙafafuna ashibta,Ya komar da ni baya,Ya bar ni a yashe, sumamme dukan yini.

Karanta cikakken babi Mak 1