Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

Mak 1:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Da dare tana kuka mai zafi,Hawaye suna zuba sharaf-sharaf a kumatunta.Dukan masoyanta ba wanda yake ta'azantar da ita.Dukan abokanta sun ci amanarta, sun zama maƙiyanta.

3. Yahuza ta tafi bauta tana shan azaba,Da bauta mai tsanani.Tana zaune a tsakiyar sauran al'umma,Amma ba ta sami hutawa ba,Gama masu runtumarta sun ci mata, ba hanyar tsira.

4. Hanyoyin Sihiyona suna baƙin cikiDomin ba mai halartar ƙayyadaddun idodi.Dukan ƙofofinta sun zama kufai,Firistocinta suna nishi,Budurwanta kuma suna wahala,Ita kanta ma tana shan wuya ƙwarai.

5. Maƙiyanta sun zama shugabanninta,Abokan gābanta kuma sun zama iyayengijinta.Gama Ubangiji ne ya sa ta sha wahalaSaboda yawan zunubanta.'Ya'yanta sun tafi bauta wurin maƙiyanta.

6. Dukan darajar Sihiyona ta rabu da ita,Shugabanninta sun zama kamar bareyinDa ba su sami wurin kiwo ba,Suna gudu ba ƙarfi a gaban wanda yake korarsu.

7. A kwanakin wahalarta na rashin wurin zama,Urushalima ta tuna da dukan abubuwanta masu daraja a dā.A lokacin da mutanenta suka fāɗa a hannun maƙiyi,Ba wanda ya taimake ta,Maƙiyanta sun gan ta,Sun yi mata ba'a saboda fāɗuwarta.

8. Urushalima ta yi zunubi ƙwarai da gaske,Saboda haka ta ƙazantu,Dukan waɗanda suka girmama ta sun raina taDomin sun ga tsiraicinta,Ita kanta ma tana nishi, ta ba da baya.

9. Ƙazantarta tana cikin tufafinta,Ba ta tuna da ƙarshenta ba,Domin haka faɗuwarta abar tsoro ce,Ba ta da mai yi mata ta'aziyya.“Ya Ubangiji, ka dubi wahalata,Gama maƙiyi ya ɗaukaka kansa!”

10. Maƙiyi ya miƙa hannunsaA kan dukan kayanta masu daraja,Gama ta ga al'ummai sun shiga Haikali,Su waɗanda ka hana su shiga cikin jama'arka.

Karanta cikakken babi Mak 1