Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 9:15-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

15. “Sai na juya, na gangaro daga dutsen da allunan nan biyu na alkawari a hannuwana, dutsen kuma na cin wuta.

16. Da na duba, sai na ga kun yi wa Ubangiji Allahnku zunubi, kun yi wa kanku maraƙi na zubi. Kun kauce da sauri daga hanyar da Ubangiji ya umarce ku ku bi.

17. Sai na ɗauki allunan nan biyu, na jefar da su ƙasa da hannuna, na farfashe su a idonku.

18. Sai na fāɗi ƙasa, na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in, ban ci ba, ban sha ba, kamar yadda na yi a dā, saboda dukan zunubin da kuka aikata, kuka yi abin da yake mugu ga Ubangiji, kuka tsokane shi.

19. Gama na ji tsoron zafin fushin Ubangiji da ya yi da ku, har ya so ya hallaka ku. Amma Ubangiji ya ji addu'ata a wannan lokaci.

20. Ubangiji kuma ya husata da Haruna, har ya so ya kashe shi, amma na yi roƙo dominsa a lokacin.

21. Sa'an nan na ɗauki abin zunubin nan, wato siffar maraƙin da kuka yi, na ƙone, na farfashe, na niƙe shi lilis, ya zama kamar ƙura mai laushi, na zubar da garin a rafi wanda yake gangarowa daga dutsen.

22. “Kun kuma tsokano Ubangiji ya husata a Tabera, da a Masaha, da a Kibrot-hata'awa.

23. Sa'ad da Ubangiji ya aike ku daga Kadesh-barneya, ya ce, ‘Ku hau ku mallaki ƙasar da nake ba ku,’ sai kuka tayar wa umarnin Ubangiji Allahnku, ba ku gaskata shi ba, ba ku kuwa yi biyayya da muryarsa ba.

24. Tun ran da na san ku, ku masu tayar wa Ubangiji ne.

25. “Sai na fāɗi na kwanta a gaban Ubangiji dare arba'in da yini arba'in saboda Ubangiji ya ce zai hallaka ku.

Karanta cikakken babi M. Sh 9