Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 4:6-11 Littafi Mai Tsarki (HAU)

6. Ku kiyaye su, ku aikata su, gama yin haka zai tabbatar wa sauran al'ummai, kuna da hikima da ganewa. Sa'ad da al'ummai za su ji waɗannan dokoki, za su ce, ‘Ba shakka, wannan babbar al'umma tana da hikima da ganewa.’

7. “Gama babu wata babbar al'umma wadda allahnta yake kusa da ita kamar yadda Ubangiji Allahnmu yake kusa da mu sa'ad da muka kira gare shi.

8. Ko kuwa, da akwai wata babbar al'umma wadda take da dokoki da farillai na adalci kamar waɗannan dokoki da na sa a gabanku yau?”

9. “Sai ku lura, ku kiyaye kanku sosai, don kada ku manta da abubuwan da kuka gani da idonku kada kuma su fita a ranku dukan kwanakinku. Ku sanar wa 'ya'yanku da jikokinku da su,

10. da yadda kuma a waccan rana kuka tsaya a gaban Ubangiji Allahnku a Horeb, sa'ad da Ubangiji ya ce mini, ‘Ka tattara mini jama'a domin su ji maganata, su koyi tsorona dukan kwanakinsu a duniya, su kuma koya wa 'ya'yansu.’

11. “Sai kuka matso kusa, kuka tsaya a gindin dutsen sa'ad da dutsten yake cin wuta har zuwa sararin sama, ga kuma girgije baƙi ƙirin yana rufe da dutsen.

Karanta cikakken babi M. Sh 4