Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 34:1-4 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Sai Musa ya tashi daga filayen Mowab zuwa Dutsen Nebo, a ƙwanƙolin Fisga wanda yake daura da Yariko. Sai Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, tun daga Gileyad har zuwa Dan,

2. da dukan Naftali, da ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, da dukan ƙasar Yahuza har zuwa Bahar Rum,

3. da Negeb, da filin kwarin Yariko, birnin itatuwan giginya, har zuwa Zowar.

4. Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”

Karanta cikakken babi M. Sh 34