Surori

  1. 1
  2. 2
  3. 3
  4. 4
  5. 5
  6. 6
  7. 7
  8. 8
  9. 9
  10. 10
  11. 11
  12. 12
  13. 13
  14. 14
  15. 15
  16. 16
  17. 17
  18. 18
  19. 19
  20. 20
  21. 21
  22. 22
  23. 23
  24. 24
  25. 25
  26. 26
  27. 27
  28. 28
  29. 29
  30. 30
  31. 31
  32. 32
  33. 33
  34. 34

Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 34 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Rasuwar Musa

1. Sai Musa ya tashi daga filayen Mowab zuwa Dutsen Nebo, a ƙwanƙolin Fisga wanda yake daura da Yariko. Sai Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, tun daga Gileyad har zuwa Dan,

2. da dukan Naftali, da ƙasar Ifraimu, da ta Manassa, da dukan ƙasar Yahuza har zuwa Bahar Rum,

3. da Negeb, da filin kwarin Yariko, birnin itatuwan giginya, har zuwa Zowar.

4. Ubangiji ya ce masa, “Wannan ita ce ƙasar da na rantse wa Ibrahim, da Ishaku, da Yakubu, zan ba da ita ga zuriyarsu. Na bar ka ka gan ta da idanunka, amma ba za ka haye, ka shiga ba.”

5. Nan fa, a ƙasar Mowab, Musa bawan Ubangiji, ya rasu kamar yadda Ubangiji ya faɗa.

6. Aka binne shi cikin kwarin ƙasar Mowab, kusa da Betfeyor, amma ba wanda ya san inda aka binne shi har yau.

7. Musa ya yi shekara ɗari da ashirin sa'ad da ya rasu. Idanunsa ba su dushe ba, ƙarfinsa kuma bai ragu ba.

8. Isra'ilawa suka yi makoki domin Musa a filayen Mowab har kwana talatin. Sa'an nan kwanakin kuka da makoki domin Musa suka ƙare.

9. Joshuwa ɗan Nun yana cike da ruhun hikima, gama Musa ya ɗibiya masa hannuwansa. Isra'ilawa suka yi masa biyayya, suka aikata bisa ga yadda Ubangiji ya umarci Musa.

10. Tun daga lokacin nan, ba a taɓa yin wani annabi a Isra'ila kamar Musa ba, wanda Ubangiji ya san shi fuska da fuska.

11. Ubangiji ya aike shi ya aikata alamu da mu'ujizai a ƙasar Masar a gaban Fir'auna da dukan barorinsa, da dukan ƙasarsa.

12. Ya kuma aikata ayyuka masu iko, masu bantsoro a gaban dukan Isra'ilawa.