Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 33:1-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Wannan ita ce albarkar da Musa, mutumin Allah, ya sa wa Isra'ilawa kafin ya rasu.

2. Ya ce,“Ubangiji ya taho daga Sina'i,Daga Dutsen Faran kuma ya haskaka,Ya taho tare da dubban tsarkakansa,Da harshen wuta a damansa.

3. Hakika, yana ƙaunar jama'arsa,Dukan tsarkaka suna a ikonka,Suna biye da kai,Suna karɓar umarninka.

4. Musa ya ba mu dokoki,Abin gādo ga taron jama'ar Yakubu.

5. Ubangiji shi ne sarki a Yeshurun,Sa'ad da shugabanni suka taru,Dukan kabilan Isra'ila suka taru.

6. “Allah ya sa Ra'ubainu ya rayu, kada ya mutu,Kada mutanensa su zama kaɗan.”

7. A kan Yahuza ya ce,“Ka ji muryar Yahuza, ya Ubangiji,Ka kawo shi wurin jama'arsa.Ka yi yaƙi da ikonka dominsu,Ka taimake shi a kan maƙiyansa.”

8. A kan Lawi ya ce,“Ka ba Mai Tsarki Tumminka da Urim naka,Shi wanda ka jarraba a Masaha,Wanda ka yi jayayya da shi a ruwan Meriba,

9. Wanda ya ce wa mahaifinsa da mahaifiyarsa,‘Ban kula da ku ba.’Ya ce wa 'yan'uwansa su ba nasa ba ne.Ya kuma ƙyale 'ya'yansa,Domin sun kiyaye maganarka,Sun riƙe alkawarinka.

10. Suna koya wa Yakubu farillanka,Suna koya wa Isra'ila dokokinka.Suna ƙona turare a gabanka,Suna ƙona hadaya ta ƙonawa a bagadenka.

11. Ya Ubangiji ka inganta jaruntakarsu,Ka karɓi aikin hannuwansu,Ka murƙushe ƙarfin abokan gābansu,Da waɗanda suke ƙinsu don kada su ƙara tashi.”

12. A kan Biliyaminu, ya ce,“Shi ƙaunatacce na Ubangiji ne,Yana zaune lafiya kusa da shi,Ubangiji yana yi masa garkuwa dukan yini,Yana zaune a kan kafaɗunsa.”

Karanta cikakken babi M. Sh 33