Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 31:19-26 Littafi Mai Tsarki (HAU)

19. “Don haka, sai ka rubuta wannan waƙa, ka koya wa Isra'ilawa. Ka sa ta a bakinsu don waƙan nan ta zama shaida a gare ni game da Isra'ilawa.

20. Sa'ad da na kawo su a ƙasar da take da yalwar abinci, wadda na rantse zan ba kakanninsu, har suka ci, suka ƙoshi, suka yi ƙiba, za su juya, su bi gumaka, su bauta musu. Za su raina ni, su tā da alkawarina.

21. Sa'ad da yawan masifun nan da wahalan nan suka same su, to, waƙar nan za ta ba da shaida a kansu, gama zuriyarsu ba za ta manta da wannan waƙa ba, gama na san ƙudurin da suke yi kafin in kawo su ƙasar da na rantse zan bayar.”

22. Saboda wannan sai Musa ya rubuta wannan waƙa a ranar, ya koya wa jama'ar Isra'ila.

23. Sai Ubangiji ya umarci Joshuwa ɗan Nun ya ce, “Ka ƙarfafa, ka yi ƙarfin hali, gama kai ne za ka kai jama'ar Isra'ila a ƙasar da na rantse zan ba su, ni kuma da kaina zan tafi tare da kai.”

24. Sa'ad da Musa ya gama rubuta maganar dokokin nan sarai a littafin,

25. sai ya umarci Lawiyawa waɗanda suke ɗaukar akwatin alkawarin Ubangiji, ya ce,

26. “Ku ɗauki littafin dokokin nan, ku ajiye shi tare da akwatin alkawari na Ubangiji Allahnku domin ya zama shaida a kanku,

Karanta cikakken babi M. Sh 31