Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 25:7-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Amma idan mutum ya ƙi ya auri matar ɗan'uwansa, marigayi, sai matar ta tafi wurin dattawa a dandalin ƙofar gari, ta ce, ‘Ɗan'uwan mijina, marigayi, ya ƙi wanzar da sunan ɗan'uwansa cikin Isra'ila, gama ya ƙi yi mini abin da ya kamaci ɗan'uwan marigayi, ya yi.’

8. Sai dattawan garin su kira mutumin, su yi masa magana. Idan ya nace, yana cewa, ‘Ba na so in aure ta,’

9. sai matar ɗan'uwansa, marigayi, ta tafi wurinsa a gaban dattawan, ta kwaɓe takalmin ƙafarsa, ta tofa masa yau a fuskarsa, ta ce, ‘Haka za a yi wa wanda ya ƙi kafa gidan ɗan'uwansa.’

10. Za a kira sunan gidansa cikin Isra'ila, ‘Gidan wanda aka kwaɓe masa takalmi.’ ”

11. “Idan mutane biyu suna faɗa da juna, idan matar mutum ɗaya daga cikinsu ta zo don ta taimaki mijinta, idan ta kama marainan wancan mutum da hannunta,

12. sai ku yanke hannunta, kada ku ji tausayi.

13. “Kada ku riƙe ma'aunin nauyi iri biyu a jakarku, wato babba da ƙarami.

14. Kada kuma ku ajiye mudu iri biyu a gidanku, wato babba da ƙarami.

15. Sai ku kasance da ma'aunin nauyi da mudu masu kyau don ku daɗe a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

16. Gama duk wanda yake aikata irin waɗannan abubuwa, da dukan marasa gaskiya, abin ƙyama ne su ga Ubangiji Allahnku.”

17. “Ku tuna da abin da Amalekawa suka yi muku a hanya, lokacin da kuka fito daga Masar.

Karanta cikakken babi M. Sh 25