Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 21:3-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Dattawan garin da ya fi kusa da gawar za su ɗauki karsana wadda ba a taɓa aiki da ita ba, ba a kuma taɓa sa mata karkiya ba.

4. Sai dattawan garin nan su kai karsanar kwari inda ruwa yake gudu, inda ba a taɓa noma ko shuka ba. A can cikin kwarin za a karya wuyan karsanar.

5. Sa'an nan sai firistoci, 'ya'yan Lawiyawa, su fito gaba, gama su ne Ubangiji Allahnku ya zaɓa don su yi masa aiki, su sa albarka da sunansa, su ne kuma masu daidaita kowace gardama da cin mutunci.

6. Sai dukan dattawan garin da ya fi kusa da gawar su wanke hannuwansu a bisa karsanar da aka karya wuyanta a kwarin.

7. Sa'an nan su ce, ‘Hannuwanmu ba su zub da wannan jini ba, idanunmu kuma ba su ga wanda ya zubar da shi ba.

8. Ya Ubangiji, ka kuɓutar da jama'arka, Isra'ila, wadda ka fansa, kada ka bar alhakin jinin marar laifin nan ya kama jama'arka, Isra'ila. Ka gafarta musu alhakin wannan jini.’

9. Ta haka za ku kawar da alhakin jinin marar laifi daga cikinku, sa'ad da kuka yi abin da yake daidai a wurin Ubangiji.”

10. “Sa'ad da kuka tafi yaƙi da magabtanku, Ubangiji Allahnku kuwa ya bashe su a hannunku, kun kuwa kama su bayi,

11. in a cikinsu ka ga wata kyakkyawar mace wadda ka yi sha'awarta, to, ka iya aurenta.

12. Sai ka kawo ta gidanka, ta aske kanta, ta yanke farcenta,

13. ta tuɓe tufafin bauta. Sa'an nan sai ta zauna a gida tana makokin mahaifinta da mahaifiyarta har wata ɗaya cif. Bayan haka ka iya shiga wurinta, ka zama mijinta, ita kuma ta zama matarka.

14. In ka ji ba ka bukatarta, sai ka sake ta ta tafi inda take so, amma kada ka sayar da ita, kada kuma ka wahalshe ta, tun da yake ka riga ka ƙasƙantar da ita.”

15. “Idan mutum yana da mata biyu, amma ya fi ƙaunar ɗayar, idan kuwa dukansu biyu, wato mowar da borar, suka haifi 'ya'ya, idan bora ce ta haifi ɗan fari,

16. to, a ranar da zai yi wa 'ya'yansa wasiyya a kan gādon da zai bar musu, kada ya sa ɗan mowa ya zama kamar shi ne ɗan fari, a maimakon ɗan borar wanda shi ne ɗan farin,

17. Amma sai ya yarda ya ba ɗan farin, wato ɗan borar, za a ba shi riɓi biyu na dukan abin da yake da shi gama shi ne mafarin ƙarfinsa, yana da hakkin ɗan fari.”

18. “Idan mutum yana da gagararren ɗa wanda ba ya jin maganar mahaifinsa da ta mahaifiyarsa, sun kuma hore shi, duk da haka bai ji ba,

19. sai mahaifinsa da mahaifiyarsa su kama shi, su kawo shi wurin dattawan garin a dandalin ƙofar gari.

20. Sai su faɗa wa dattawan garinsu, su ce, ‘Wannan ɗanmu ne, gagararre, ba ya yi mana biyayya. Shi mai zari ne, mashayi!’

Karanta cikakken babi M. Sh 21