Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 14:10-24 Littafi Mai Tsarki (HAU)

10. Kada ku ci duk irin abin da ba shi da ƙege ko ɓamɓaroki, gama haram yake a gare ku.

11. “Kuna iya cin dukan halattattun tsuntsaye.

12. Amma waɗannan tsuntsaye ne ba za ku ci ba, mikiya, da gaggafa, da ungulun kwakwa,

13. da duki, da buga zabi, da kowace irin shirwa,

14. da kowane irin hankaka,

15. da jimina, da ƙururu, da bubuƙuwa, da kowane irin shaho,

16. da mujiya, da babbar mujiya, da ɗuskwi,

17. da kwasakwasa, da ungulu, da dimilmilo,

18. da zalɓe, da kowane irin jinjimi, da katutu, da yaburbura.

19. “Dukan 'yan ƙwari masu fikafikai masu rarrafe haram ne a gare ku, kada ku ci su.

20. Za ku iya cin duk abin da yake da fikafikai in dai shi halattacce ne.

21. “Kada ku ci mushe. Amma mai yiwuwa ne ku ba baren da yake zaune a garuruwanku, ko kuma ku sayar wa baƙo. Gama ku jama'a ce keɓaɓɓiya ga Ubangiji Allahnku.“Kada ku dafa ɗan akuya a madarar uwarsa.”

22. “Ku fitar da zakar dukan amfanin da kuka shuka a gonarku kowace shekara.

23. Ku ci zakar sabon hatsinku, da ruwan inabinku, da manku, da 'yan fari na shanunku, da tumakinku, a gaban Ubangiji Allahnku, a wurin da zai zaɓa ya tabbatar da sunansa, don ku koyi tsoron Ubangiji Allahnku har abada.

24. Idan ya zamana wurin ya yi muku nisa, har ba za ku iya kai zakar a wurin ba, saboda wurin da Ubangiji Allahnku ya zaɓa domin ya tabbatar da sunansa ya yi muku nisa sa'ad da Ubangiji Allahnku ya sa muku albarka,

Karanta cikakken babi M. Sh 14