Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Sh 13:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. “Idan wani annabi, ko mai mafarki ya fito a cikinku, ya yi muku shelar wata alama ko mu'ujiza,

2. idan alamar ko mu'ujizar ta auku, idan kuma ya ce, ‘Bari mu bi gumaka, mu bauta musu, gumakan da ba ku san su ba,

3. kada ku saurari maganar annabin nan ko mai mafarkin nan, gama Ubangiji Allahnku yana jarraba ku ne, ya gani, ko kuna ƙaunarsa da zuciya ɗaya da dukan ranku.

4. Sai ku bi Ubangiji Allahnku, ku yi tsoronsa, ku kiyaye umarnansa, ku kasa kunne ga muryarsa, shi ne za ku bauta masa, ku manne masa kuma.

5. Sai a kashe annabin nan, ko mai mafarkin don ya koyar a tayar wa Ubangiji Allahnku wanda ya fisshe ku daga ƙasar Masar, wato inda kuka yi bauta, gama ya yi ƙoƙari ya sa ku ku kauce daga hanyar da Ubangiji Allahnku ya umarce ku ku bi. Ta haka za ku kawar da mugunta daga cikinku.

6. “Idan ɗan'uwanka, wato ɗan mahaifiyarka, ko ɗanka, ko 'yarka, ko ƙaunatacciyar matarka, ko amininka ya rarrashe ka a asirce, yana cewa, ‘Bari mu tafi mu bauta wa gumaka waɗanda ku da ubanninku ba ku san su ba,’

7. wato gumakan al'umman da suke kewaye da ku, ko suna kusa da ku, ko suna nesa da ku, daga wannan bangon duniya zuwa wancan,

8. kada ku yarda, kada ku saurare shi. Kada kuma ku ji tausayinsa, kada ku haƙura da shi ko ku ɓoye shi.

Karanta cikakken babi M. Sh 13