Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

M. Had 7:3-19 Littafi Mai Tsarki (HAU)

3. Baƙin ciki ya fi dariya,Gama baƙin ciki yakan kawo gyara.

4. Mai hikima yakan yi tunanin mutuwa,Amma wawa yakan yi tunanin shagalin duniya.

5. Gara mutum ya ji tsautawar mai hikima,Da ya ji wawaye suna yabonsa.

6. Dariyar wawa kamar ƙarar ƙayar da take karce gindin tukunya ce.Wannan ma aikin banza ne.

7. Hakika zalunci yakan sa mai hikima ya zama wawa,Karɓar rashawa kuma yakan lalata hali.

8. Gara ƙarshen abu da farkonsa.Mai haƙuri kuma ya fi mai girmankai.

9. Ka kame fushinka,Gama wawa ne yake cike da fushi.

10. Kada ka yi tambaya, cewa me ya sa zamanan dā suka fi na yanzu?Gama wannan tambaya ba ta hikima ba ce.

11. Ya kamata kowane mutum ya zama mai hikima,Gama tana da kyau kamar cin gādo.

12. Hikima mafaka ce, takan kāre mutum kamar yadda kuɗi yake yi.Kiyayewar da hikima takan yi wa mai ita, ita ce amfanin ilimi.

13. Ka yi tunanin aikin Allah,Wa ya isa ya miƙe abin da ya tanƙware?

14. In kana jin daɗi, ka yi murna,In kuma wahala kake sha, ka tuna,Allah ne ya yi duka biyunsa,Don kada mutum ya san abin da zai faru a nan gaba.

15. A kwanakina marasa amfani na ga kowane irin abu. Adali ba safai yakan yi tsawon rai ba, mugu kuwa yakan yi tsawon rai a mugayen ayyukansa.

16. Kada ka cika yin adalci, kada kuma ka cika yin hikima, gama don me za ka kashe kanka?

17. Kada ka cika yin mugunta, kada kuma ka cika yin wauta, gama don me za ka mutu tun kwanakinka ba su cika ba?

18. Idan ka riƙe wannan zai amfane ka. Kada ka bar wancan, gama shi wanda yake tsoron Allah zai yi amfani da su.

19. Abin da hikima take iya yi wa mutum ɗaya ya fi abin da masu mulki goma za su yi wa birni.

Karanta cikakken babi M. Had 7