Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 9:45-51 Littafi Mai Tsarki (HAU)

45. Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri.

46. Da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji labari, suka gudu zuwa hasumiyar gidan Ba'al-berit don su tsira.

47. Abimelek kuwa ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru wuri ɗaya.

48. Sai ya tafi da mutanen da suke tare da shi suka hau Dutsen Zalmon. Ya ɗauki gatari ya sari reshen itace, ya saɓe a kafaɗa. Ya ce wa mutanen da suke tare da shi, su yi hanzari su yi kamar yadda ya yi.

49. Kowane mutum kuwa ya sari reshen itace, ya bi Abimelek. Suka tara rassan a jikin hasumiyar. Suka sa wa hasumiyar wuta, duk da mutanen da suke cikinta. Ta haka dukan mutanen hasumiyar Shekem suka mutu, mata da maza, wajen mutum dubu.

50. Sa'an nan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta da sansani, ya ci birnin.

51. Akwai wata hasumiya mai ƙarfi a cikin birnin, sai dukan mutanen garin, mata da maza, har da shugabannin, suka gudu zuwa cikinta, suka kulle kansu, suka hau kan rufin hasumiyar.

Karanta cikakken babi L. Mah 9