Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 9:44-57 Littafi Mai Tsarki (HAU)

44. Abimelek kuma da ƙungiyar da take tare da shi, suka hanzarta, suka tsare ƙofar birnin. Sauran ƙungiya biyu suka ruga, suka faɗa wa dukan waɗanda suke cikin saura, suka karkashe su.

45. Abimelek ya yi yaƙi dukan yini har ya ci birnin, ya kashe mutanen da suke cikinsa. Ya rushe birnin, ya barbaɗe shi da gishiri.

46. Da shugabannin hasumiyar Shekem suka ji labari, suka gudu zuwa hasumiyar gidan Ba'al-berit don su tsira.

47. Abimelek kuwa ya ji dukan mutanen hasumiyar Shekem sun taru wuri ɗaya.

48. Sai ya tafi da mutanen da suke tare da shi suka hau Dutsen Zalmon. Ya ɗauki gatari ya sari reshen itace, ya saɓe a kafaɗa. Ya ce wa mutanen da suke tare da shi, su yi hanzari su yi kamar yadda ya yi.

49. Kowane mutum kuwa ya sari reshen itace, ya bi Abimelek. Suka tara rassan a jikin hasumiyar. Suka sa wa hasumiyar wuta, duk da mutanen da suke cikinta. Ta haka dukan mutanen hasumiyar Shekem suka mutu, mata da maza, wajen mutum dubu.

50. Sa'an nan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta da sansani, ya ci birnin.

51. Akwai wata hasumiya mai ƙarfi a cikin birnin, sai dukan mutanen garin, mata da maza, har da shugabannin, suka gudu zuwa cikinta, suka kulle kansu, suka hau kan rufin hasumiyar.

52. Abimelek kuwa ya zo ya yaƙi hasumiyar. Ya je kusa da ƙofar hasumiyar don ya ƙone ta.

53. Amma wata mace ta jefi Abimelek da ɗan dutsen niƙa a kā, ƙoƙon kansa ya ragargaje.

54. Nan da nan sai Abimelek ya kira saurayin da yake ɗaukar masa makamai, ya ce masa, “Ka zaro takobinka, ka kashe ni domin kada mutane su ce, ‘Mace ta kashe shi.’ ” Sai saurayin ya soki Abimelek, ya mutu.

55. Da Isra'ilawa suka ga Abimelek ya mutu, sai dukansu suka tafi gida.

56. Ta haka Allah ya saƙa wa Abimelek muguntar da ya yi wa mahaifinsa, da ya kashe 'yan'uwansa maza, su saba'in.

57. Haka kuwa Allah ya sa muguntar mutanen Shekem ta koma kansu. Bakin Yotam, ɗan Yerubba'al, kuma ya kama su.

Karanta cikakken babi L. Mah 9