Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 9:32-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

32. Yanzu sai ka tashi, ka zo da dare tare da mutanen da suke tare da kai, ku yi kwanto a cikin saura.

33. Sa'an nan gobe da safe, da fitowar rana, ku tashi ku fāɗa wa birnin. Idan Ga'al da mutanen da suke tare da shi, suka fito, su kara da kai, ka fatattake su yadda ka iya!”

34. Abimelek da mutanen da suke tare da shi kuwa suka tashi da dare suke yi wa Shekem kwanto da ƙungiya huɗu.

35. Ga'al, ɗan Ebed, kuwa ya fita zuwa ƙofar garin daidai lokacin da Abimelek da mutanensa suka tashi daga wurin kwantonsu.

36. Sa'ad da Ga'al ya ga mutanen, ya ce wa Zebul, “Duba, ga mutane suna zuwa daga kan duwatsu.”Sai Zebul ya ce masa, “Ai, inuwar duwatsu ce kake gani kamar mutane.”

37. Ga'al kuma ya ƙara yin magana, ya ce, “Duba, mutane suna gangarowa kan hanya, ga kuma wata ƙungiya tana zuwa daga wajen itacen oak na masu duba.”

38. Sa'an nan Zebul ya ce masa, “Ina cika bakin nan naka, kai da ka ce, ‘Wane ne Abimelek da za mu bauta masa?’ Waɗannan su ne mutanen da ka raina. Fita, ka yaƙe su mana.”

39. Ga'al kuwa ya fita ya yi jagorar shugabannin Shekem, suka yi yaƙi da Abimelek.

Karanta cikakken babi L. Mah 9