Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 6:13-25 Littafi Mai Tsarki (HAU)

13. Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al'ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, ‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar’? Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.”

14. Ubangiji ya ce masa, “Tafi da dukan ƙarfinka, ka ceci Isra'ilawa daga Madayanawa. Ni kaina na aike ka.”

15. Gidiyon ya amsa ya ce, “Ubangiji, yaya zan yi in ceci Isra'ilawa? Ga shi, dangina ne mafi ƙanƙanta a kabilar Manassa, ni ne kuma ƙarami a gidanmu.”

16. Ubangiji kuwa ya ce masa, “Za ka iya, gama zan taimake ka. Za ka muttsuke Madayanawa kamar mutum guda.”

17. Gidiyon kuwa ya ce masa, “Idan ka amince da ni, ka nuna mini alama don in sani kai kake magana da ni.

18. Ina roƙonka, kada ka tashi daga nan, sai na kawo maka hadaya ta abinci.”Ya amsa cewa, “Zan tsaya har ka kawo.”

19. Gidiyon ya tafi gida, ya yanka ɗan akuya, ya dafa, ya yi waina marar yisti ta gāri mudu guda. Ya sa naman a kwandon, romon kuwa ya zuba a tukunya, ya kawo, ya miƙa masa a gindin itacen oak.

20. Mala'ikan Allah kuma ya ce masa, “Ɗauki naman da wainar marar yisti ka sa a kan dutsen nan, sa'an nan ka zuba romon a kai.” Haka kuwa ya yi.

21. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya miƙa kan sandan da yake hannunsa, ya taɓa naman da wainar, sai wuta ta fito daga dutsen ta cinye naman da wainar. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya ɓace masa.

22. Da Gidiyon ya gane mala'ikan Ubangiji ne, sai ya ce, “Kaitona, Ubangiji Allah, gama na ga mala'ikan Ubangiji fuska da fuska.”

23. Amma Ubangiji ya ce masa, “Kada ka ji tsoro, ba za ka mutu ba.”

24. Gidiyon kuwa ya gina wa Ubangiji bagade a wurin, ya sa masa suna, Ubangiji Salama Ne. Har wa yau bagaden yana nan a Ofra, ta iyalin Abiyezer.

25. A wannan dare Ubangiji ya ce masa, “Ka ɗauki bijimin mahaifinka, da wani bijimin bana bakwai. Sa'an nan ka rushe bagaden gunkin nan Ba'al na mahaifinka, ka sare gumakan da suke kusa da shi.

Karanta cikakken babi L. Mah 6