Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 6:1-13 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Jama'ar Isra'ila kuma suka sāke yin zunubi a gaban Ubangiji, sai Ubangiji ya ba da su ga Madayanawa su mallake su shekara bakwai.

2. Madayanawa kuwa sun fi Isra'ilawa ƙarfi, saboda haka Isra'ilawa suka yi ta ɓuya a kogon dutse, da waɗansu wuraren ɓuya a tsaunuka.

3. Duk lokacin da Isra'ilawa suka yi shuka, sai Madayanawa, da Amalekawa, da waɗansu kabilai na hamada su zo su fāɗa musu.

4. Sukan zo su kafa musu sansani, su ɓaɓɓata amfanin ƙasar har zuwa kusa da Gaza. Ba su barin wani abinci a ƙasar Isra'ila, domin Isra'ilawa ko dabbobinsu.

5. Gama sukan zo da dabbobinsu da alfarwansu da yawa, kamar fara. Su da raƙumansu ba su ƙidayuwa, sukan zo, su lalatar da ƙasar.

6. Isra'ilawa suka sha ƙasƙanci ƙwarai a hannun Madayanawa. Sai suka yi kuka ga Ubangiji domin ya taimake su.

7. Da Isra'ilawa suka yi kuka ga Ubangiji saboda wahalar da Madayanawa suke ba su,

8. sai Ubangiji ya aika musu da wanda ya faɗa musu saƙon Ubangiji, Allah na Isra'ila, ya ce, “Ni ne na fito da ku daga bauta a Masar.

9. Na cece ku daga Masarawa, da kuma waɗanda suka yi yaƙi da ku a nan. Na kore su a gabanku, na ba ku ƙasarsu.

10. Na faɗa muku, ‘Ni ne Ubangiji Allahnku, kada ku bauta wa gumakan Amoriyawa, waɗanda kuke zaune a ƙasarsu.’ Amma ba ku yi biyayya da maganata ba.”

11. Mala'ikan Ubangiji ya zo, ya zauna a gindin itacen oak na Yowash mutumin Abiyezer, a ƙauyen Ofra. Ɗansa Gidiyon kuwa yana susukar alkama daga ɓoye, a wurin da ake matse ruwan inabi, don ya ɓuya daga Madayanawa.

12. Mala'ikan Ubangiji kuwa ya bayyana gare shi, ya ce, “Kai jarumi ne, Ubangiji kuma yana tare da kai.”

13. Sai Gidiyon ya ce masa, “Ya shugabana, idan Ubangiji yana tare da mu, me ya sa abubuwan nan suka same mu? Ina kuma ayyukansa masu ban al'ajabi waɗanda kakanninmu suka faɗa mana cewa, ‘Ai, Ubangiji ne ya fisshe mu daga Masar’? Amma yanzu Ubangiji ya yi watsi da mu, ya ba da mu ga Madayanawa.”

Karanta cikakken babi L. Mah 6