Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 4:7-12 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ni kuwa zan jawo Sisera, shugaban sojojin Yabin, da karusansa, da ƙungiyoyin sojojinsa ya yi karo da kai a Kogin Kishon, zan kuwa bashe shi a hannunka.’ ”

8. Barak ya ce mata, “Idan za ki tafi tare da ni, zan tafi, amma idan ba za ki tafi tare da ni ba, ni ma ba zan tafi ba.”

9. Sai ta ce masa, “Hakika zan tafi tare da kai, amma darajar wannan tafiya ba za ta zama taka ba, gama Ubangiji zai ba da Sisera a hannun mace.” Debora kuwa ta tashi, ta tafi tare da Barak zuwa Kedesh.

10. Barak kuwa ya kirawo kabilar Zabaluna da ta Naftali zuwa Kedesh. Mutum dubu goma (10,000) suka rufa masa baya, Debora kuwa ta haura tare da shi.

11. Eber, Bakene kuwa, ya ware daga Keniyawa, zuriyar Hobab, surukin Musa, ya kafa alfarwarsa can nesa wajen oak a Za'anannim wanda yake kusa da Kedesh.

12. Aka faɗa wa Sisera cewa, Barak ɗan Abinowam ya haura zuwa Dutsen Tabor.

Karanta cikakken babi L. Mah 4