Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 21:7-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

7. Ƙaƙa za mu yi don mutanen da suka ragu su sami mata. Ga shi, mum riga mu rantse da Ubangiji ba za mu ba su 'ya'yanmu mata su aura ba?”

8. Sa'an nan suka ce, “Wace kabila ce daga cikin kabilar Isra'ila ba ta hauro zuwa wurin Ubangiji a Mizfa ba?.. Sai suka ga, ashe, ba wani daga Yabesh-gileyad da ya halarci taron.

9. Gama sa'ad da aka tattara mutanen, aka ga ba wani daga cikin mazaunan Yabesh-gileyad a wurin.

10. Taron jama'a kuma suka aiki jarumawansu mutum dubu goma sha biyu (12,000) zuwa Yabesh-gileyad. Suka umarce su cewa, “Ku je ku karkashe mazaunan Yabesh duka har da mata da yara.

11. Abin da za ku yi ke nan, ku je ku kashe dukan maza, da kowace mace wadda ba budurwa ba ce.”

12. Suka sami budurwai ɗari huɗu daga mutanen Yabesh-gileyad, sai suka kawo su zango a Shilo, wadda take a ƙasar Kan'ana.

13. Sa'an nan taron jama'a suka aika wa mutanen Biliyaminu da suke a Dutsen Rimmon, cewa, yaƙi ya ƙare, sai salama.

14. Mutanen Biliyaminu kuwa suka komo, aka ba su budurwan nan da aka bar su da rai aka kawo su Yabesh-gileyad, amma budurwan ba su ishe su ba.

15. Sai mutanen suka yi juyayin mutanen Biliyaminu domin Ubangiji ya naƙasa kabila daga kabilar Isra'ila.

16. Saboda haka dattawan taron jama'a suka ce, “Ƙaƙa za mu yi da waɗanda suka ragu da ba su sami mata ba, da yake an hallaka matan kabilar Biliyaminu?”

17. Sai suka ce, “Tilas, waɗanda suka ragu daga mutanen Biliyaminu su sami gādo domin kada a shafe kabila daga cikin Isra'ila,

18. amma fa ba za mu iya aurar musu da 'ya'yanmu mata ba.” Sun faɗi haka ne kuwa, domin sun riga sun rantse cewa, “Duk wanda ya aurar da 'yarsa ga mutumin Biliyaminu la'ananne ne.”

19. Suka kuma ce, “Ga shi, idin Ubangiji na shekara shekara a Shilo ya kusa.” (Shilo tana arewacin Betel, kudu da Lebona, gabas da hanyar da take tsakanin Betel da Shekem.)

20. Suka umarci mutanen Biliyaminu suka ce, “Ku tafi ku yi kwanto a gonakin inabi,

Karanta cikakken babi L. Mah 21