Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 20:35-43 Littafi Mai Tsarki (HAU)

35. Ubangiji kuwa ya fatattake mutanen Biliyaminu a gaban Isra'ilawa. Isra'ilawa kuwa suka hallaka mutanen Biliyaminu dubu ashirin da biyar da ɗari ɗaya (25,100) a wannan rana, waɗannan duka kuwa mayaƙa ne.

36. Mutanen Biliyaminu kuwa suka gane an ci su da yaƙi.Mutanen Isra'ila kuwa suka yi ta ja da baya daga mutanen Biliyaminu domin sun dogara ga mutanensu da suka yi wa Gibeya kwanto.

37. Sai 'yan kwanto suka gaggauta suka faɗa wa Gibeya, suka kutsa suka kashe dukan waɗanda suke a birnin.

38. Alamar da mayaƙan Isra'ila da na 'yan kwantonsu suka daidaita a tsakaninsu, ita ce murtukewar hayaƙi a cikin birnin.

39. Idan mutanen Isra'ila sun hangi hayaƙin, sai su juya su fāɗa wa mutanen Biliyaminu da yaƙi. Kafin alamar hayaƙin sai mutanen Biliyaminu suka fara kashe wa Isra'ilawa wajen mutum talatin. Suka ce, “Ai, suna shan ɗibga a hannunmu kamar yadda suka sha da fari.”

40. Amma sa'ad da alamar hayaƙin ta fara murtukewa a cikin birnin, sai mutanen Biliyaminu suka juya, suka duba, suka ga hayaƙi ya murtuke cikin birnin, ya yi sama.

41. Da mutanen Isra'ila suka juyo kansu, sai mutanen Biliyaminu suka tsorata, gama sun ga masifa ta auko musu.

42. Don haka suka juya suka kama gudu suka nufi hamada, amma ba su tsira ba. Aka datse su tsakanin 'yan kwanto da sauran sojojin Isra'ilawa.

43. Suka yi wa mutanen Biliyaminu tarko, suka runtume su ba tsayawa tun daga Menuha har zuwa daura da Gibeya daga gabas.

Karanta cikakken babi L. Mah 20