Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 14:2-10 Littafi Mai Tsarki (HAU)

2. Sa'ad da ya hauro zuwa gida sai ya faɗa wa iyayensa, ya ce, “Na ga ɗaya daga cikin 'yan matan Filistiyawa a Timna, ina so ku auro mini ita.”

3. Amma iyayensa suka ce masa, “Cikin 'yan'uwanka da mutanenka duka, ba yarinyar da za ka aura daga cikin 'yan matansu, har ka tafi ka auro mace daga na Filistiyawa marasa kaciya?”Amma Samson ya ce wa mahaifinsa, “Ita ce wadda nake bukata, ka auro mini ita. Ina sonta.”

4. Iyayensa ba su san al'amarin nan daga wurin Ubangiji ne ba, gama Ubangiji yana so wannan ya zama sanadin yaƙi da Filistiyawa, gama a lokacin nan Filistiyawa ne suke mulkin Isra'ilawa.

5. Samson kuwa ya gangara zuwa Timna, shi da iyayensa. Da ya isa gonakin inabin Timna, sai ga sagarin zaki ya taso masa da ruri.

6. Ruhun Ubangiji kuwa ya sauko a kansa da iko, sai ya yaga zakin da hannu, kamar yadda akan yayyage ɗan akuya. Amma bai faɗa wa iyayensa abin da ya yi ba.

7. Sa'an nan ya gangara ya yi zance da budurwar, yana kuwa sonta.

8. Bayan 'yan kwanaki sai ya koma don ya auro ta. Ya ratse don ya duba gawar zakin da ya kashe, sai ya tarar da cincirindon ƙudan zuma, da kuma zuma a cikin gawar zakin, ya yi mamaki.

9. Ya ɗebo zuman a hannunsa, yana tafe yana sha, har ya isa wurin iyayensa, ya ba su, suka sha, amma bai faɗa musu daga cikin gawar zaki ya ɗebo zuman ba.

10. Mahaifinsa ya tafi gidan iyayen yarinyar, Samson kuma ya shirya liyafa a can, gama haka samari sukan yi.

Karanta cikakken babi L. Mah 14