Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 14:11-20 Littafi Mai Tsarki (HAU)

11. Sa'ad da Filistiyawa suka gan shi suka sa samari talatin su zauna tare da shi.

12. Samson kuwa ya ce musu, “Bari in yi muku ka-cici-ka-cici, idan kun faɗa mini amsarsa a kwana bakwai na bikin, to, zan ba ku rigunan lilin talatin da waɗansu riguna talatin na ado.

13. Amma idan kun kāsa ba ni amsar, to, ku ne za ku ba ni rigunan lilin talatin da waɗansu rigunan na ado.”Sai suka ce, “To, faɗi ka-cici-ka-cicin mu ji.”

14. Sai ya ce musu,“Daga mai ci, abinci ya fito,Daga kuma mai ƙarfi, zaƙi ya fito.”Ba su iya ba da amsar ba har kwana uku.

15. A rana ta huɗu suka ce wa matar Samson, “Ki rarrashi mijinki ya gaya mana amsar ka-cici-ka-cicin, idan kuwa kin ƙi, to, za mu ƙone ki da gidan mahaifinki da wuta. Kun gayyace mu don ku tsiyata mu ne?”

16. Sai matar Samson ta yi kuka a gabansa tana cewa, “Kai dai maƙiyina ne, ba masoyina ba, ka yi wa mutanena ka-cici-ka-cici, amma ba ka gaya mini amsarsa ba.”Amma ya ce mata, “Ko iyayena ma ban faɗa musu ba, sai in faɗa miki?”

17. Ta kuwa yi ta yi masa kuka har rana ta bakwai ta ƙarewar bikinsu. Amma a rana ta bakwai, ya faɗa mata amsar saboda yawan fitinarta. Ita kuwa ta faɗa wa mutanenta amsar ka-cici-ka-cicin.

18. A rana ta bakwai, kafin rana ta faɗi, mutanen garin suka ce masa,“Me ya fi zuma zaƙi?Me kuma ya fi zaki ƙarfi?”Ya kuwa ce musu,“Da ba don kun haɗa baki da matata ba,Da ba ku san amsar ka-cici-ka-cicin ɗin nan ba.”

19. Sa'an nan Ruhun Ubangiji ya sauko a kansa da iko, ya gangara zuwa Ashkelon. Ya kashe mutum talatin a can, ya kwashe ganima, ya ba waɗanda suka faɗa masa amsar ka-cici-ka-cicin riguna. Ya koma gida a husace saboda abin da ya faru.

20. Aka ɗauki matar Samson aka ba wanda ya yi masa abokin ango.

Karanta cikakken babi L. Mah 14