Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 13:4-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

4. Yanzu sai ki lura, kada ki sha ruwan inabi, ko abin sha mai gāfi, kada kuma ki ci haramtaccen abu,

5. gama za ki yi juna biyu, ki haifi ɗa. Ba za ki taɓa aske kansa ba Zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki. Shi ne zai ceci Isra'ilawa daga hannun Filistiyawa.”

6. Macen kuwa ta tafi ta faɗa wa mijinta cewa, “Mutumin Allah ya zo wurina, fuskarsa tana da bantsoro kamar fuskar mala'ikan Ubangiji. Ni kuwa ban tambaye shi inda yake ba, shi kuma bai faɗa mini sunansa ba.

7. Amma ya ce mini, zan yi juna biyu, in haifi ɗa, don haka kada in sha ruwan inabi, ko abin sa maye, kada kuma in ci haramtaccen abu, gama yaron zai zama keɓaɓɓe ga Allah tun daga cikin ciki har zuwa ranar da zai rasu.”

8. Sa'an nan Manowa ya yi roƙo ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangijina, ina roƙonka ka bar mutumin Allah wanda ka aiko, ya sāke zuwa wurinmu, ya faɗa mana abin da za mu yi wa yaron da za a haifa.”

Karanta cikakken babi L. Mah 13