Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 10:1-3 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan mutuwar Abimelek, sai Tola, ɗan Fuwa, ɗan Dodo, daga kabilar Issaka ya tashi don ya ceci Isra'ilawa. Ya zauna a Shamir, a ƙasar tuddai ta Ifraimu.

2. Ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da uku, sa'an nan ya rasu. Aka binne shi a Shamir.

3. Bayansa kuma sai Yayir mutumin Gileyad, ya tashi ya shugabanci Isra'ilawa shekara ashirin da biyu.

Karanta cikakken babi L. Mah 10