Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 1:5-17 Littafi Mai Tsarki (HAU)

5. Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan'aniyawa da Ferizziyawa.

6. Sai Adoni-bezek ya gudu, amma suka bi shi, suka kama shi. Suka yanyanke manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.

7. Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.

8. Mutanen Yahuza kuwa suka yaƙi Urushalima, suka ci ta, suka karkashe mutanenta, suka kuma cinna mata wuta.

9. Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari.

10. Suka kuma tafi su yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a Hebron wadda a dā ake kira Kiriyat-arba. Suka kashe Sheshai, da Ahiman, da Talmai.

11. Daga can suka tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer.

12. Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.”

13. Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi 'yarsa Aksa aure.

14. Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”

15. Sai ta amsa masa, “Ka yi mini alheri, da yake ka tura ni a ƙasar Negeb, ka ba ni maɓuɓɓugan ruwa.” Kalibu kuwa ya ba ta maɓuɓɓugan tuddai da na kwari.

16. Zuriyar Bakene, surukin Musa kuwa suka fita tare da mutanen Yahuza daga birnin dabino, wato Yariko, suka tafi jejin Yahuda da take a Negeb kudu da Arad. A can suka zauna tare da Amalekawa.

17. Yahuza kuwa da ɗan'uwansa, Saminu, suka tafi suka bugi Kan'aniyawan da suke zaune a Zefat. Suka la'anta birnin, suka hallaka shi, suka sāke wa birnin suna Horma, wato hallakarwa.

Karanta cikakken babi L. Mah 1