Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Mah 1:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Bayan da Joshuwa ya rasu, jama'ar Isra'ila suka tambayi Ubangiji suka ce, “Wane ne daga cikinmu zai fara tafiya don ya yaƙi Kan'aniyawa?”

2. Sai Ubangiji ya ce, “Yahuza ne zai tafi, ga shi, na ba da ƙasar a gare shi.”

3. Yahuza kuwa ya ce wa Saminu ɗan'uwansa, “Ka zo tare da ni a wurin da aka ba ni rabon gādona don mu yaƙi Kan'aniyawa, ni kuma zan tafi tare da kai a wurin da aka ba ka rabon gādonka.” Saminu ya tafi tare da shi.

4. Yahuza ya tafi, Ubangiji kuwa ya ba da Kan'aniyawa da Ferizziyawa a gare su, suka kashe mutum dubu goma daga cikinsu a Bezek.

5. Suka iske Adoni-bezek a can, suka yi yaƙi da shi, suka kuma ci Kan'aniyawa da Ferizziyawa.

6. Sai Adoni-bezek ya gudu, amma suka bi shi, suka kama shi. Suka yanyanke manyan yatsotsinsa na hannu da na ƙafa.

7. Ya kuma ce, “Sarakuna saba'in waɗanda aka yanyanke manyan yatsotsinsu na hannu da na ƙafa, suka kalaci abincinsu a ƙarƙashin teburina. Allah kuwa ya yi mini kamar yadda na yi musu.” Suka kawo shi Urushalima, a nan ya mutu.

8. Mutanen Yahuza kuwa suka yaƙi Urushalima, suka ci ta, suka karkashe mutanenta, suka kuma cinna mata wuta.

9. Bayan wannan suka gangara kuma, suka yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a ƙasar tudu, da Negeb, da filayen kwari.

10. Suka kuma tafi su yaƙi Kan'aniyawan da suke zaune a Hebron wadda a dā ake kira Kiriyat-arba. Suka kashe Sheshai, da Ahiman, da Talmai.

11. Daga can suka tafi su yaƙi Debir wadda a dā ake kira Kiriyat-Sefer.

12. Kalibu ya ce, “Duk wanda ya fāɗa wa Kiriyat-Sefer da yaƙi har ya ci ta, zan ba shi 'yata Aksa aure.”

13. Sai Otniyel ɗan Kenaz, ƙanen Kalibu ya ci birnin da yaƙi, Kalibu kuwa ya ba shi 'yarsa Aksa aure.

14. Da ta zo wurinsa, ta iza shi ya roƙi mahaifinta saura. Da ta sauka daga kan jakinta, sai Kalibu ya ce mata, “Me kike so?”

Karanta cikakken babi L. Mah 1