Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 6:1-8 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji kuma ya umarci Musa

2. ya faɗa wa Isra'ilawa, cewa idan mace ko namiji ya ɗau wa'adi na musamman na zama keɓaɓɓe domin ya keɓe kansa ga Ubangiji,

3. sai ya keɓe kansa daga ruwan inabin da yake sa maye da ruwan inabi mai tsami. Kada kuma ya sha ruwan inabi mai tsami da yake sa maye da kowane irin abin sha da aka yi da 'ya'yan inabi mai tsami. Kada kuma ya ci ɗanyu ko busassun 'ya'yan inabi.

4. A dukan kwanakin nan da ya keɓe kansa, kada ya ci kowane irin abu da aka yi da kurangar inabi, ko da ƙwayar inabi ko da ɓawonsa.

5. A dukan kwanakin wa'adinsa na keɓewa, kada aska ta taɓa kansa, sai kwanakin keɓewar kansa ga Ubangiji sun cika. Zai zama mai tsarki, zai kuma bar sumarsa ta yi tsawo.

6. A dukan kwanakin da ya keɓe kansa ga Ubangiji, kada ya kusaci gawa.

7. Ko ta mahaifinsa ce, ko ta mahaifiyarsa, ko ta ɗan'uwansa, ko ta 'yar'uwarsa, ba zai ƙazantar da kansa ba, tun da yake ya keɓe kansa ga Allahnsa.

8. Shi tsattsarka ne ga Ubangiji dukan kwanakin da ya keɓe kansa.

Karanta cikakken babi L. Kid 6