Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 4:24-49 Littafi Mai Tsarki (HAU)

24. Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi wajen ɗaukar kaya.

25. Za su ɗauki alfarwa ta sujada, da labule na ciki da na waje, da murfi na fatun tumaki wanda yake a bisa alfarwar, da kuma labulen ƙofar alfarwa ta sujada,

26. da labulen farfajiya, da labulen ƙofar farfajiya wadda ta kewaye alfarwar da bagaden, da igiyoyinsu, da duk kayayyakinsu na yin aiki. Sai su yi dukan abin da ya kamata a yi da su.

27. Haruna ne da 'ya'yansa maza za su nuna wa 'ya'yan Gershonawa irin aikin da za su yi, da kayayyakin da za su ɗauka. Sai a faɗa musu dukan abin da za su yi, da dukan abinda za su ɗauka.

28. Wannan shi ne aikin da iyalan Gershonawa za su yi a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi zai shugabance su cikin aikin da za su yi.

29. Ubangiji kuma ya faɗa wa Musa ya ƙidaya Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu,

30. ya rubuta su tun daga mai shekara talatin, har zuwa mai shekara hamsin, duk wanda ya isa yin aikin da zai yi a alfarwa ta sujada.

31. Wannan shi ne abin da aka umarce su su riƙa ɗauka na wajen aikinsu a alfarwa ta sujada, katakan alfarwar, da sandunanta, da dirkokinta, da kwasfanta,

32. da dirkokin farfajiya wadda take kewaye da alfarwar, da kwasfansu, da turakunsu, da igiyoyi, da dukan kayayyakinsu. Sai ya faɗa wa kowa kayan da zai ɗauka.

33. Wannan shi ne aikin iyalan 'ya'yan Merari, maza. Aikinsu ke nan duka a alfarwa ta sujada. Itamar ɗan Haruna, firist, shi ne zai shugabance su.

34-48. Musa da Haruna da shugabannin taron jama'a kuwa suka ƙidaya iyalan Lawiyawa uku, wato Kohatawa, da Gershonawa da Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, aka rubuta dukan mazaje daga mai shekara talatin zuwa mai shekara hamsin, waɗanda za su iya aiki a alfarwa ta sujada, kamar haka, Kohat dubu biyu da ɗari bakwai da hamsin (2,750), Gershon dubu biyu da ɗari shida da talatin (2,630), Merari dubu uku da ɗari biyu (3,200), Jimilla duka, dubu takwas da ɗari biyar da tamanin (8,580).

49. Aka ba kowannensu aikinsa da ɗaukar kaya bisa ga umarnin da Ubangiji ya yi wa Musa. Haka kuwa aka ƙidaya su kamar yadda Ubangiji ya umarci Musa.

Karanta cikakken babi L. Kid 4