Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 4:34-48 Littafi Mai Tsarki (HAU)

Musa da Haruna da shugabannin taron jama'a kuwa suka ƙidaya iyalan Lawiyawa uku, wato Kohatawa, da Gershonawa da Merariyawa bisa ga iyalansu da gidajen kakanninsu, aka rubuta dukan mazaje daga mai shekara talatin zuwa mai shekara hamsin, waɗanda za su iya aiki a alfarwa ta sujada, kamar haka, Kohat dubu biyu da ɗari bakwai da hamsin (2,750), Gershon dubu biyu da ɗari shida da talatin (2,630), Merari dubu uku da ɗari biyu (3,200), Jimilla duka, dubu takwas da ɗari biyar da tamanin (8,580).

Karanta cikakken babi L. Kid 4

gani L. Kid 4:34-48 a cikin mahallin