Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 29:33-40 Littafi Mai Tsarki (HAU)

33. Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

34. Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

35. A rana ta takwas za a taru domin yin sujada. Ba za a yi aiki ba.

36. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi, da rago, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin su zama marasa lahani.

37. Za a miƙa hadaya ta gāri da hadaya ta sha tare da bijimin, da ragon, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

38. Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

39. Waɗannan su ne hadayun da za a miƙa wa Ubangiji a lokacin idodinsu, duk da hadayunsu na wa'adi, da na yardar rai, da na ƙonawa, da na gāri, da na sha, da na salama.

40. Musa kuwa ya faɗa wa jama'ar Isra'ila kome da kome kamar yadda Ubangiji ya umarce shi.

Karanta cikakken babi L. Kid 29