Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 29:29-39 Littafi Mai Tsarki (HAU)

29. A rana ta shida ta idin za a miƙa bijimai takwas, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

30. Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

31. Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya taƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

32. A rana ta bakwai ta idin za a miƙa bijimai bakwai, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya. Dabbobin su zama marasa lahani.

33. Za a kuma miƙa hadaya ta gāri da hadayu na sha tare da bijiman, da ragunan, da 'yan ragunan bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

34. Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

35. A rana ta takwas za a taru domin yin sujada. Ba za a yi aiki ba.

36. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi, da rago, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin su zama marasa lahani.

37. Za a miƙa hadaya ta gāri da hadaya ta sha tare da bijimin, da ragon, da 'yan ragunan, bisa ga adadinsu, da kuma bisa ga ka'idar.

38. Za a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, duk da hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri da hadayarta ta sha.

39. Waɗannan su ne hadayun da za a miƙa wa Ubangiji a lokacin idodinsu, duk da hadayunsu na wa'adi, da na yardar rai, da na ƙonawa, da na gāri, da na sha, da na salama.

Karanta cikakken babi L. Kid 29