Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 29:1-14 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. A rana ta fari ga wata na bakwai za a taru domin yin sujada, ba za a yi aiki a ranar ba. A ranar za a busa ƙahoni.

2. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi guda, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin za su zama marasa lahani.

3. Tare da dabbobin za a kuma miƙa hadaya ta lallausan gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimin, humushi biyu na garwa kuma tare da ragon.

4. Za a miƙa humushin garwa na gāri tare da kowane ɗan rago.

5. Sai kuma a miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi domin a yi kafara.

6. Banda waɗannan hadayu kuma, sai a miƙa hadaya ta ƙonawa tare da hadayarta ta gari, da akan yi a tsayawar wata, da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha. Sai a yi su bisa ga ka'idar yinsu. Hadaya ke nan da akan yi da wuta don daɗin ƙanshi ga Ubangiji.

7. Za a yi tsattsarkan taro a rana ta goma ga watan bakwai domin yin sujada. Ba za a ci abinci ba, ba kuwa za a yi aiki ba.

8. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da bijimi ɗaya, da rago guda, da 'yan raguna bakwai bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani.

9. Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta gāri kwaɓaɓɓe da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da ragon,

10. da humushin garwa kuma tare da kowane ɗan rago.

11. Za a kuma miƙa bunsuru guda saboda hadaya don zunubi, banda hadaya don zunubi saboda yin kafara, da hadaya ta ƙonawa ta kullum, tare da hadayarta ta gāri, da hadayarsu ta sha.

12. A rana ta goma sha biyar ga watan bakwai za a yi tsattsarkan taro domin yin sujada, ba za a yi aiki ba. Su kiyaye idin da girmama Ubangiji har kwana bakwai.

13. Za a miƙa hadaya ta ƙonawa da 'yan bijimai goma sha uku, da raguna biyu, da 'yan raguna goma sha huɗu bana ɗaya ɗaya don daɗin ƙanshi ga Ubangiji. Dabbobin nan su zama marasa lahani.

14. Tare da dabbobin za a miƙa hadaya ta lallausan gāri wanda aka kwaɓa da mai. Za a miƙa gāri humushi uku na garwa tare da kowane bijimi, da gāri humushi biyu na garwa tare da kowane rago,

Karanta cikakken babi L. Kid 29