Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 19:1-9 Littafi Mai Tsarki (HAU)

1. Ubangiji ya yi magana da Musa da Haruna, ya ce,

2. “Wannan ita ce ka'ida wadda Ubangiji ya umarta. Ka faɗa wa Isra'ilawa su kawo maka jar karsana, marar lahani, wadda ba ta da wani aibi, wadda ba a taɓa aza mata karkiya ba.

3. Sai ka ba Ele'azara firist ita, sa'an nan a kai ta bayan sansani, a yanka ta gabansa.

4. Ele'azara, firist, kuwa zai ɗibi jininta da yatsansa, ya yayyafa sau bakwai a wajen alfarwar ta sujada.

5. Sai a ƙone karsanar a idonsa, za a ƙone fatarta, da naman, da jinin, tare da tarosonta.

6. Firist zai ɗauki itacen al'ul, da ɗaɗɗoya, da mulufi, ya jefa a wutar da take ƙone karsanar.

7. Sai firist ɗin ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, sa'an nan ya shiga zangon. Firist ɗin zai ƙazantu har zuwa maraice.

8. Shi kuma wanda ya ƙone karsanar, sai ya wanke tufafinsa, ya yi wanka da ruwa, shi ma zai ƙazantu har zuwa maraice.

9. Mutumin da yake da tsarki shi zai tara tokar karsanar, ya ajiye a wuri mai tsabta a bayan zangon. Za a adana tokar domin jama'ar Isra'ila, za a riƙa zubawa a ruwa don tsarkakewar zunubi.

Karanta cikakken babi L. Kid 19