Tsohon Alkawari

Sabon Wasiya

L. Kid 18:25-32 Littafi Mai Tsarki (HAU)

25. Ubangiji ya ce wa Musa,

26. “Har yanzu ka faɗa wa Lawiyawa, cewa sa'ad da suka karɓi zaka daga Isra'ilawa wadda na ba su gādo, sai su fitar da zaka daga cikin zakar, su miƙa wa Ubangiji hadaya ta ɗagawa.

27. Za a lasafta hadayarku ta ɗagawa kamar hatsinku ne da kuka sussuka a masussuka, da kuma kamar cikakken amfanin ruwan inabin da kuka samu a wurin matsewar inabinku.

28. Haka za ku miƙa hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji daga cikin dukan zakar da kuke karɓa daga wurin Isra'ilawa. Daga ciki za ku ba da hadaya ta ɗagawa ga Ubangiji ta hannun Haruna, firist.

29. Daga dukan kyautar da ake kawo muku, za ku ba Ubangiji hadaya ta ɗagawa daga mafi kyau da kuke samu.

30. Domin haka kuwa sai ka ce musu, ‘Sa'ad da kuka ɗaga mafi kyau daga cikinta duka, sai ragowar ta zama ta Lawiyawa kamar abin da ya fito daga masussuka, da wurin matsewar inabinsu.

31. Za ku iya cinta ko'ina da kuka ga dama, ku da iyalan gidajenku, gama ladanku ke nan saboda aikin da kuke yi a alfarwa ta sujada.

32. Ba kuwa za ta zama muku sanadin zunubi ba, in dai har kuka ɗaga mafi kyau duka. Ba za ku ɓata tsarkakakkun abubuwa na Isra'ilawa ba, don kada ku mutu.’ ”

Karanta cikakken babi L. Kid 18